L. Fir 15:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.

16. Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

17. Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

L. Fir 15