L. Fir 13:57-59 Littafi Mai Tsarki (HAU)

57. Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar.

58. Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abin da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa'ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.

59. Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.

L. Fir 13