L. Fir 13:37-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Amma idan a ganinsa mikin bai yaɗu ba, baƙin gashi ya tsiro ya kuma yi tsawo a wurin, mikin ya warke ke nan, mutumin ya tsarkaka, firist kuwa zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.

38. Idan a fatar jikin mace ko namiji akwai fararen tabbai,

39. sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne.

L. Fir 13