L. Fir 11:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Namansu kuma zai zama abin ƙyama a gare ku, ba za ku ci ba. Mushensu kuma abin ƙyama ne.

12. Kowane irin abin da yake cikin ruwa da ba shi da ƙege da kamɓori, abin ƙyama ne a gare ku.

13. Za ku ji ƙyamar waɗannan irin tsuntsaye, ba za ku ci su ba, gama abin ƙyama ne su, wato, gaggafa, da mikiya, da ungulun kwakwa,

14. da shirwa, da buga zabi, da irinsu,

15. da kowane irin hankaka,

16. da jimina, da mujiya, da shaho, da irinsu,

17. da ƙururu, da babba da jaka, da zarɓe,

18. da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu,

19. da shamuwa, da jinjimi da irinsa, da burtu, da jemage.

20. Dukan ƙwarin da yake da fikafikai ƙazantattu ne,

21. sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

22. Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu.

L. Fir 11