K. Mag 8:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku kasa kunne! Hikima tana kira.Tana so a ji ta.

2. Tana tsaye bisa kan tuddai a bakin hanyaDa a mararraban hanyoyi.

3. A ƙofofin shiga birni, tana kira,

4. “Ina roƙonku, ya ku, 'yan adam,Ina kiran kowane mutum da yake a duniya.

5. Ba ku balaga ba? To, ku balaga.Ku wawaye ne? Ku koyi hankali.

6. Ku kasa kunne ga jawabina mafi kyau,Dukan abin da na faɗa muku daidai ne.

K. Mag 8