11. Za ku kwanta kuna nishi a kan gadon mutuwa, namanku da tsokokinku za su zagwanye.
12. Sa'an nan za ku ce, “Me ya sa ban taɓa koyo ba? Me ya sa ban yarda wani ya kwaɓe ni ba?
13. Ban kasa kunne ga malamaina ba. Ban mai da hankalina gare su ba.
14. Farat ɗaya sai aka kunyatar da ni a bainar jama'a.”
15. Ka yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta ita kaɗai.
16. Idan kuma waɗansu mata sun haifa maka 'ya'ya, 'ya'yan nan ba za su yi maka wani amfani ba.
17. 'Ya'yanka za su yi girma su taimake ka, ba na baƙi ba.