K. Mag 31:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Takan samo ulu da lilin, ta yi saƙa da hannuwanta da farin ciki.

14. Takan kawo abincinta daga nesa, kamar fatake.

15. Takan yi asubanci ta shirya wa iyalinta abinci, ta kuma shirya wa 'yan matan gidanta aike-aiken da za su yi.

16. Takan lura da gona sosai kafin ta saya, da ribar da ta ci take dasa gonar inabi.

17. Takan himmantu ta yi aiki tuƙuru.

18. Ta sani akwai riba a cikin kasuwancinta. Fitilarta na ci dare farai.

19. Da hannunta take kaɗi, tana kuma saƙa da hannuwanta.

20. Takan yi wa matalauta da masu fatara karamci.

21. Ba ta jin tsoron lokacin sanyi gama 'ya'yanta duka suna da tufafi masu ƙauri.

22. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa, tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

23. Mijinta sananne ne a dandali, sa'ad da yake zaune tare da dattawan gari.

K. Mag 31