10. Wa yake iya samun cikakkiyar mace? Darajarta ta fi ta lu'ulu'ai.
11. Mijinta yakan amince da ita, ba kuwa zai yi hasara ba.
12. Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakinta.
13. Takan samo ulu da lilin, ta yi saƙa da hannuwanta da farin ciki.
14. Takan kawo abincinta daga nesa, kamar fatake.
15. Takan yi asubanci ta shirya wa iyalinta abinci, ta kuma shirya wa 'yan matan gidanta aike-aiken da za su yi.