17. Ka hori ɗanka zai daɗaɗa maka rai, ya kuma faranta maka zuciya.
18. Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.
19. Bara ba ya horuwa ta wurin magana kawai, gama ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
20. Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
21. Baran da aka shagwaɓa tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa tankar magājin gida.
22. Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.
23. Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.
24. Abokin ɓarawo mugun maƙiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce kome ba.
25. Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.
26. Mutane da yawa sukan nemi farin jini daga wurin mai mulki, amma Ubangiji ne yake yi wa mutum adalci.
27. Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga adali, adali kuma abin ƙyama ne ga mugun.