K. Mag 28:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.

18. Ka yi aminci za ka zauna lafiya, idan kuwa ka yi rashin aminci za ka fāɗi.

19. Manomin da yake aiki sosai, zai sami wadataccen abinci, amma mutanen da suke zaman banza ko yaushe, za su zama matalauta.

20. Amintaccen mutum zai cika kwanakinsa lafiya, amma idan kana so ka sami dukiya dare ɗaya, za a hukunta ka.

21. Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda 'yar ƙaramar rashawa.

22. Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.

K. Mag 28