K. Mag 28:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Mutumin da yake tsoron Ubangiji ko yaushe, zai yi farin ciki, amma idan ya taurare zai lalace.

15. Talakawa ba su da wani taimako sa'ad da suke ƙarƙashin mulkin mugun. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanɗa.

16. Mai mulki wanda ba shi da basira yakan zama mai mugun tsanani. Amma wanda yake ƙin rashin aminci, ko ta ƙaƙa zai daɗe yana mulki.

17. Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.

18. Ka yi aminci za ka zauna lafiya, idan kuwa ka yi rashin aminci za ka fāɗi.

19. Manomin da yake aiki sosai, zai sami wadataccen abinci, amma mutanen da suke zaman banza ko yaushe, za su zama matalauta.

K. Mag 28