K. Mag 25:26-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Mutumin kirki wanda yakan yarda da mugun yana tunasshe ka da ƙazantattun maɓuɓɓuga ko rijiya mai dafi.

27. Kamar yadda shan zuma da yawa ba shi da kyau a gare ka, haka kuma ƙoƙarin neman yabo mai yawa yake.

28. Idan ba ka iya danne fushinka ba, ka zama mai kasala kamar birnin da ba shi da garuka, yana buɗe don a faɗa masa.

K. Mag 25