K. Mag 24:27-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Kada ka gina gidanka ka kafa shi, sai ka gyara gonakinka, ka tabbata za ka sami abin zaman gari.

28. Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isasshen dalili ba, ko ka faɗi ƙarya a kansa.

29. Kada ka ce, “Zan yi masa daidai da yadda ya yi mini, zan rama masa!”

30. Na ratsa ta gonakin inabin wani malalaci, dakiki,

31. suna cike da ƙayayuwa, ciyayi sun sha kansu, katangar dutse da take kewaye da su ta faɗi.

32. Da na dubi wannan, na yi tunani a kansa, ya zamar mini ishara.

K. Mag 24