1. Kada ka ji ƙyashin mugaye, kada ka yi ƙoƙarin yin abuta da su.
2. Duk tunaninsu na yin mugunta ne, a duk lokacin da suka buɗe bakinsu sai sun cuci wani.
3. An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi.
4. Ta wurin ilimi a kan ƙawata ɗakuna da kyawawan kayayyaki masu tamani.
5. Mai hikima ƙaƙƙarfa ne, i, mai ilimi yana daɗa ƙarfi.
6. Banda wannan ma, dole ne ka shisshirya a natse kafin ka kama yaƙi. Bisa ga shawarwarin da za ka samu ne za ka yi nasara.
7. Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa'ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.
8. Idan a ko yaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali.
9. Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama'a suna ƙin mutum mai rainako.