6. Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.
7. Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.
8. In ka shuka rashin gaskiya masifa ce za ta tsiro, wato hukunci mai tsanani wanda zai hallakar da kai.
9. Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.
10. Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.
11. In ka yi ladabi za ka zama aminin sarki, gama yana ƙaunar amintaccen mutum.
12. Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.
13. Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”
14. Zina tarko ce, takan kama waɗannan waɗanda Ubangiji yake fushi da su.
15. Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.