K. Mag 22:24-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai.

25. Mai yiwuwa ne ka koyi irin ɗabi'unsu, har ka kasa sākewa.

26. Kada ka yi alkawarin ɗaukar wa wani lamuni,

27. gama idan ka kāsa biya har gadonka ma za su ɗauke.

28. Kada ka kawar da shidar kan iyaka wadda kakanninka suka kafa.

K. Mag 22