K. Mag 22:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Idan ya zama dole ne ka zaɓa tsakanin kyakkyawan suna ko dukiya, to, ka zaɓi kyakkyawan suna, tagomashi kuma ya fi azurfa da zinariya.

2. Ba bambanci tsakanin mawadaci da matalauci, gama Ubangiji ne ya halicce su duka.

3. Mutum mai hankali, in ya ga wahala tana zuwa yakan kauce mata, amma shashasha yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.

4. Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali'u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.

5. Idan kana ƙaunar ranka ka nisanci tarkunan da aka kafa a hanya don su kama mugaye.

6. Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.

7. Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.

8. In ka shuka rashin gaskiya masifa ce za ta tsiro, wato hukunci mai tsanani wanda zai hallakar da kai.

9. Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.

10. Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.

11. In ka yi ladabi za ka zama aminin sarki, gama yana ƙaunar amintaccen mutum.

12. Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.

K. Mag 22