K. Mag 20:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. 'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.

8. Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.

9. Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?

10. Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.

11. Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.

12. Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.

13. Idan barci ne sana'arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.

14. Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.

15. In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.

16. Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.

17. Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.

K. Mag 20