K. Mag 2:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa.

7. Shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci.

8. Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.

9. Idan ka kasa kunne gare ni za ka san abin da yake daidai, da abin da yake gaskiya, da abin da yake na kirki. Za ka san abin da za ka yi.

10. Za ka zama mai hikima, iliminka zai faranta maka rai.

11. Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka.

12. Za su hana ka aikata mugayen ayyuka, za su nisantar da kai daga mutane masu ta da hargitsi da irin maganganunsu,

13. mutane waɗanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi,

14. waɗanda suke jin daɗin yin laifi, suna nishaɗi cikin mugunta.

15. Ba za a dogara da su ba, ba kuwa za a iya amincewa da su ba.

16. Za a nisantar da kai daga mazinaciya, wadda take ƙoƙari ta lalatar da kai da daɗin bakinta,

17. marar aminci ga mijinta, wadda ta manta da tsarkakan alkawaran da ta ɗauka.

K. Mag 2