K. Mag 15:19-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko'ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.

20. Ɗa mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa.

21. Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da yake daidai.

K. Mag 15