K. Mag 11:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto.

10. Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa'ad da mugaye suka mutu.

11. Biranen da adalai suke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.

K. Mag 11