K. Mag 11:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.

14. Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.

15. Wanda ya ɗaukar wa baƙo lamuni zai yi da na sani, zai fi maka sauƙi idan ba ruwanka.

16. Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su sami dukiya.

K. Mag 11