12. Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la'akari yakan kame bakinsa.
13. Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.
14. Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.
15. Wanda ya ɗaukar wa baƙo lamuni zai yi da na sani, zai fi maka sauƙi idan ba ruwanka.
16. Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su sami dukiya.
17. In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar.
18. A ainihi mugaye ba su cin ribar kome, amma idan ka yi abin da yake daidai, ka tabbata za a sāka maka da alheri.