K. Mag 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Karin maganar Sulemanu, ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila.

2. Ga Karin magana da za su taimake ka ka rarrabe da hikima, da kyakkyawar shawara, da fahimtar ma'anar zurfafan karin magana,

3. da yadda za ka karɓi koyarwa ta hanyar hikima, da adalci, da gaskiya, da sanin abin da yake daidai.

4. Sukan sa marar sani ya zama masani, sukan koya wa samari yadda za su zama masu amfani.

5. Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana,

K. Mag 1