Josh 8:21-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sa'ad da Joshuwa da dukan Isra'ilawa suka ga 'yan kwanto sun ci birnin, da kuma hayaƙi ya murtuke bisa, suka juya kan mutanen Ai, suka ɗibge su.

22. Sauran Isra'ilawa kuwa suka fito daga cikin birnin suka fāɗa musu. Har ya zama suna tsakiyar Isra'ilawa gaba da baya. Isra'ilawa suka karkashe su, har ba wanda ya tsira ko ya tsere.

23. Amma suka kama Sarkin Ai da rai, suka kai shi wurin Joshuwa.

24. Sa'ad da Isra'ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra'ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta.

25. A wannan rana aka ƙarasa mutanen Ai duka, mata da maza. Jimillarsu ta kai mutum dubu goma sha biyu (12,000).

26. Joshuwa bai janye hannunsa da riƙon mashin ba, sai da ya hallaka mazaunan Ai sarai.

27. Dabbobi da kayayyaki na birnin kaɗai Isra'ilawa suka kwashe ganima bisa ga faɗar Ubangiji zuwa ga Joshuwa.

28. Haka fa Joshuwa ya ƙone Ai, ya maishe ta tsibin kufai har abada. Tana nan haka har wa yau.

29. Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa'ad da rana take faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau.

30. Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra'ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal.

Josh 8