1. Amma Isra'ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
2. Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.