Josh 18:20-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Kogin Urdun shi ne iyakar a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Biliyaminu suka gāda.

21. Biranen iyalan kabilar Biliyaminu ke nan Yariko, da Bet-hogla, da Emekkeziz,

22. da Bet-araba, da Zemarayim, da Betel,

23. da Awwim, da Fara, da Ofra,

24. da Kefar-ammoni, da Ofni, da Geba. Birane goma sha biyu ke nan tare da ƙauyukansu.

25. Akwai kuma Gibeyon, da Rama, da Biyerot,

26. da Mizfa, da Kefira, da Moza,

27. da Rekem, da Irfeyel, da Tarala,

28. da Zela, da Elef, da Yebus, wato Urushalima, da Gebeya, da Kiriyat. Birane goma sha huɗu ke nan tare da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon mutanen Biliyaminu bisa ga iyalansu.

Josh 18