Ish 9:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu,Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi.Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al'ummarDa ta zalunci jama'arka, ta kuma zambace su,Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni.

5. Takalman sojojin da suka kawo yaƙiDa dukan tufafinsu da suka birkiɗe da jini,Za a ƙone su da wuta!

6. Ga shi, an haifa mana ɗa!Mun sami yaro!Shi zai zama Mai Mulkinmu.Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,”“Allah Maɗaukaki,”“Uba Madawwami,”“Sarkin Salama.”

7. Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba,Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin,Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa,Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.

Ish 9