22. za su ba da isasshiyar madarar da za ta biya dukan bukatarsa. Hakika dukan waɗanda suka ragu a ƙasar za su sami yawan albarka su ƙoshi.
23. “A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.
24. Ba wanda yake da ƙarfin hali da zai iya tafiya can, sai ko wanda yake da kwari da baka. Hakika ƙasar duka za ta cika da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa.
25. Dukan tuddai inda dā akan shuka amfanin gona, za su cika da ƙayayuwa, har da ba mai iya zuwa wurin. Zai zama wurin kiwon shanu da tumaki.”