1. Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.
2. Labari ya kai gun Sarkin Yahuza, cewa sojojin Suriya sun shiga ƙasar Isra'ila. Sai shi da dukan jama'arsa suka firgita ƙwarai, suna ta kaɗuwa kamar itatuwan da iska take kaɗawa.
3. Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Ka ɗauki ɗanka Sheyar-yashub ka je ka sami sarki Ahaz. Za ka same shi a hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a wajen ƙarshen wuriyar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake sama da ita.