Ish 66:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali'u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.

3. “Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.

4. Saboda haka zan aukar musu da masifa, ainihin abin da suke jin tsoro, gama ba wanda ya amsa sa'ad da na yi kira, ko ya kasa kunne sa'ad da na yi magana. Suka zaɓa su yi mini rashin biyayya, su kuma aikata mugunta.”

5. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga 'yan'uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba'a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!

6. Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!

7. “Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba.

Ish 66