Ish 57:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Rabonku yana cikin duwatsu masu sulɓi na cikin kwari. A gare su kuka kwarara hadaya ta sha, kuka kawo hadaya ta gari. Kuna tsammani zan ji daɗin waɗannan al'amura?

7. A kan dogayen duwatsu masu tsayi kuka sa gadonku. A can kuka haura don ku miƙa hadaya.

8. A bayan ƙofa da madogaran ƙofa kuka kafa gumakanku. Kun rabu da ni, kun kware gadonku, kuna hau kun fāɗaɗa shi, kuka ƙulla yarjejeniya tsakaninku da su. Kuna ƙaunar gadonsu, kun dubi tsiraici.

Ish 57