Ish 57:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala'i.

2. Ya shiga da salama yana hutawa a kabarinsa, shi wanda ya yi tafiya da adalci.

3. Amma ku ku matso nan kusa, ku 'ya'ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa.

Ish 57