5. Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.
6. Ɗaukakarsa za ta inuwantar da birnin daga zafin rana, ta sa ya zama lafiyayyen wurin da aka kāre daga ruwan sama da hadiri.