Ish 29:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Dukan al'ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro.

9. Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba!

10. Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.

11. Za a ɓoye muku ma'anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake.

12. In kuwa kun ba wanda bai iya karatu ba, kuka roƙe shi ya karanta muku, zai ce bai iya karatu ba.

Ish 29