5. A wahayin na ga an shirya biki, an shisshimfiɗa darduma inda waɗanda aka gayyata za su zauna. Suna ci suna sha. Farat ɗaya sai aka ji umarni cewa, “Jarumawa! Ku shirya garkuwoyinku.”
6. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sa mai tsaro, ka faɗa masa ya riƙa ba da labarin abin da ya gani.
7. Idan ya ga mutane biyu biyu suna zuwa a kan dawakai, waɗansu kuma a kan raƙuma da jakuna, ka faɗa masa ya lura da su sosai.”