Ish 12:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce,“Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni,Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.

2. Allah ne Mai Cetona,Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba.Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi,Shi ne Mai Cetona.”

Ish 12