5. Amma ba su kasa kunne ba, ba su kuwa ji ba, da za su juyo daga mugayen ayyukansu na miƙa wa gumaka hadayu.
6. Saboda haka fushina ya yi zafi a kan garuruwan Yahuza da titunan Urushalima, don haka a yanzu sun lalace, suka zama kufai.
7. “Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?
8. Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la'ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya.