Irm 36:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'ad da Mikaiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji da take a littafin,

12. sai ya gangara gidan sarki, ya shiga ɗakin magatakarda, inda dukan shugabanni suke zaune, wato Elishama magatakarda, da Delaiya ɗan Shemaiya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemariya ɗan Shafan, da Zadakiya ɗan Hananiya, da dukan sarakuna.

13. Sai Mikaiya ya faɗa musu dukan maganar da ya ji sa'ad da Baruk ya karanta littafin a kunnuwan jama'a.

14. Sai dukan sarakunan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya faɗa wa Baruk ya kawo littafin nan da ya karanta wa jama'a. Sai Baruk ɗan Neriya ya ɗauki littafin ya je wurinsu.

15. Suka ce masa ya zauna, ya karanta musu littafin. Baruk kuwa ya karanta musu.

16. Da suka ji dukan maganar, suka dubi juna a firgice, suka ce wa Baruk, “Ai, sai mu faɗa wa sarki wannan magana.”

17. Suka kuma tambayi Baruk, suka ce, “Ka faɗa mana yadda ka yi ka rubuta wannan magana. Ya yi maka shibta ne?”

18. Sai Baruk ya ce musu, “Ya yi mini shibtar dukan wannan magana ne, na kuwa rubuta su da tawada a takarda.”

19. Sarakunan kuwa suka ce wa Baruk, “Ka tafi, da kai da Irmiya ku ɓuya kada ku bari kowa ya san wurin da kuke.”

20. Suka tafi zauren sarki bayan sun ajiye littafin a ɗakin Elishama, magatakarda, suka sanar da sarki dukan abin da yake cikin littafin.

21. Sarki ya aiki Yehudi ya je ya kawo littafin. Sai ya je ya ɗauko littafin daga ɗakin Elishama magatakarda. Yehudi kuwa ya karanta wa sarki tare da dukan sarakunan da suke tsaye kewaye da sarkin.

22. A watan tara ne, sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, ga wuta tana ci cikin kasko a gabansa.

Irm 36