Irm 32:23-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.

24. “Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.

25. Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”

26. Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya,

27. “Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.

28. Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin.

29. Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi.

30. Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.

31. Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.

32. Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.

Irm 32