21. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima,
22. ‘Za a kwashe su a kai Babila, a can za su kasance har lokacin da zan sāke kulawa da su. Sa'an nan ne zan komo da su, in maishe su a wannan wuri.’ ”