sa'an nan ne sarakuna waɗanda za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda, za su shiga ta ƙofofin wannan birni, suna hawan karusai, da dawakai, su da sarakunansu, da jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima. Za a zauna a wannan birni har abada.