1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ba za ka yi aure ka haifi 'ya'ya mata da maza a wannan wuri ba.
3. Ga abin da ni Ubangiji na faɗa a kan 'ya'ya mata da maza da aka haifa a wannan wuri, da kuma a kan iyayensu mata da maza da suka haife su a wannan ƙasa,