Irm 10:6-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya Ubangiji, ba wani kamarka,Kai mai girma ne,Sunanka kuma yana da girma daiko.

7. Wane ne ba zai ji tsoronka ba, yaSarkin dukan al'ummai?Ka isa a ji tsoronka,Gama babu kamarka a cikin dukanmasu hikima na al'ummai,Da kuma cikin dukan mulkokinsu,Ba wani kamarka.

8. Dukansu dakikai ne wawaye,Koyarwar gumaka ba wani abu bane, itace ne kawai!

9. An kawo fallayen azurfa dagaTarshish,Da zinariya kuma daga Ufaz,Aikin gwanaye da maƙeranzinariya.Tufafinsu na mulufi ne da shunayya,duka aikin gwanaye.

10. Amma Ubangiji shi ne Allah nagaskiya,Shi Allah mai rai ne,Shi Sarki ne madawwami.Saboda hasalarsa duniya ta girgiza,Al'ummai ba za su iya jurewa dafushinsa ba.

11. Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”

12. Shi ne, ta wurin ikonsa ya yi duniya,Ta wurin hikimarsa ya kafa ta,Ta wurin basirarsa kumaya ya shimfiɗasammai.

13. Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙuginruwa a cikin sammaiYakan kawo ƙasashi daga ƙurewarduniya,Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwansama,Daga cikin taskokinsa yakan kawoiska.

14. Kowane mutum dakiki ne, mararilimi,Kowane maƙerin zinariya zai shakunya saboda gumakansa,Gama siffofinsa ƙarya ne,Ba numfashi a cikinsu.

15. Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne,A lokacin da za a hukunta su za sulalace.

16. Gama shi ba kamar waɗannan yakeba,Shi na Yakubu ne.Shi ne ya yi dukan kome,Kabilan Isra'ilawa gādonsa,Sunansa Ubangiji Mai Runduna.

17. Ku tattara kayayyakinku,Ku mazaunan wurin da aka kewayeda yaƙi.

18. Gama haka Ubangiji ya ce,“Ga shi, ina jefar da mazaunanƙasar daga ƙasarsu a wannanlokaci,Zan kawo musu wahala, za su kuwaji jiki.”

19. Tawa ta ƙare, saboda raunin da akayi mini.Raunina mai tsanani ne,Amma na ce, lalle wannan azaba ce,Tilas in daure da ita.

20. An lalatar da alfarwata,Dukan igiyoyi sun tsintsinke,'Ya'yana maza sun bar ni, ba sunan.Ba wanda zai kafa mini alfarwataYa kuma rataya labulena.

21. Makiyayan dakikai ne,Ba su roƙi Ubangiji ba,Don haka ba su sami wadata ba,An watsa dukan garkensu.

22. Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shikuma, yana tafe.Akwai babban hargitsin da ya fitodaga arewa,Don a mai da biranen Yahuza kufai,wurin zaman diloli.

Irm 10