Irm 10:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku.

2. Ubangiji ya ce,“Kada ku koyi abubuwan daal'ummai suke yi,Kada ku ji tsoron alamun da suke asama,Ko da yake al'ummai suna jintsoronsu.

3. Gama al'adun mutane na ƙarya ne,Daga cikin jeji aka sare wani itace,Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi dagizago.

4. Mutane sukan yi masa ado na azurfada zinariya,Sukan ɗauki guduma su kafa shi daƙusoshi,Don kada ya motsa.

Irm 10