20. Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.
21. In kuwa ka ƙi sakin jama'ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama'arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.
22. A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama'ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya.
23. Zan sa iyaka tsakanin jama'ata da jama'arka. Gobe ne wannan mu'ujiza za ta auku.”’
24. Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir'auna, da gidan fādawansa, da ko'ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.