3. Amma zan taurare zuciyar Fir'auna don in aikata alamu da mu'ujizai cikin ƙasar Masar.
4. Amma Fir'auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama'ata, wato Isra'ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko.
5. Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra'ilawa daga tsakiyarsu.”
6. Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.
7. Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku sa'ad da suka yi magana da Fir'auna.
8. Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
9. “Idan Fir'auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al'ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir'auna. Sandan kuwa zai zama maciji.”
10. Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir'auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji.
11. Fir'auna kuwa ya kirawo shahararrun malamai, da masu sihiri, su kuma su yi haka ta wurin sihirinsu na Masarawa.
12. Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.