19. Sa'an nan ya shimfiɗa murfi a bisa alfarwa ya rufe alfarwar kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
20. Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin a bisansa.
21. Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa'an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
22. Musa ya sa teburin cikin alfarwa ta sujada, a wajen gefen arewa na alfarwa, a gaban labulen.
23. Sa'an nan ya jera gurasa daki-daki a bisa teburin a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
24. Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa.