3. Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Sai ya jefa shi ƙasa, sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya yi gudunsa.
4. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka ka kama wutsiyarsa.” Ya miƙa hannunsa ya kama shi, ya zama sanda kuma a hannunsa.
5. Sai Ubangiji ya ce, “Ta haka za su gaskata Ubangiji Allah na kakanninsu ne, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya bayyana gare ka.”
6. Sai Ubangiji ya sāke ce masa, “Sa hannunka cikin ƙirjinka.” Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannunsa a kuturce fari fat.
7. Allah kuma ya ce masa, “Mai da hannunka cikin ƙirjinka.” Sai ya mai da hannunsa cikin ƙirjinsa. Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa.