1. Ya kuma yi bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba'i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.
2. Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu. Zankayen a haɗe suke da shi. Ya dalaye bagaden da tagulla.
3. Da tagulla ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.
4. Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya.